Itace sabuwar hanyar gudanar da harkokin saye da sayarwa a
shafukan yanar gizo cikin ilimin fasahar sadarwa ta zamani. Ta hanyar
kasuwancin zamani za’a iya aiwatar da sana’o’i masu yawan gaske. Anan zamu
bayyana kadan daga cikin sana’o’in da’ake gudanarwa a yanar gizo.
Gina Shafukan Yanar gizo (Web design):
Wannan zai’iya zama matakin farko, saboda sai an samar da
shafukan yanar gizo kafin har akai ga gudanar da sana’o’I ko wadansu al’amura a
yanar gizo. Misali: Idan muka duba kasuwannin mu na zahiri za muga cewa anyi
musu tsari da gine-ginen manya da kanan shaguna ko runfuna wadanda ‘yan kasuwa
suke baje kolen hajojinsu ko sana’ar su a ciki.
Saboda haka sana’ar bude ko gina shafin yanar gizo na da
daraja ta farko wajen samar da bigire ko dandalin kasuwanci da sauran al’amura
masu yawan gaske.
Kamar yadda sana’ar dillanci take a kasuwannin mu na zahiri
haka take a yanar gizo. Sannan kuma ta kasance daya daga cikin manyan sana’o’i
da matsayi fiye da yadda mai karatu yake tsammani. Ana iya diilancin gidaje,
hajoji, karatuttuka, kamfanoni da sauran su duk acikin yanar gizo.
Ana bibiyar dillalai har shafukansu na yanar gizo domin basu
aikin da suka saba. Har a yanar gizo dillalai sun kasance masu kwazo da hikima
wajen shigar da duk irin hajar da aka basu dillanci. Kuma ana basu kamasho mai
tsoka a duk kasuwancin da suka gudanar. Idan har dillanci shine sana’ar ka kuma
Allah yasa kana da ilimin zamani to aikai sarkine a duniyar gizo.
Dillali zai bude shafi a yanar gizo ya fara tallata kansa
ma’ana sana’arsa, yayi cikakken bayanin irin hikimar da Allah ya hore masa,
yadda zai ja hankulan manyan kamfanonin yanar gizo. Kuma idan har ya sami aiki
ko hajar siyarwa to a wadannan shafukan nasa zai karkasasu kowa ya gani ya kuma
kara masu daraja cikin kalamai masu daukar hankalin mai saye har a sami nasara.
Ana iya dillancin maziyarta ma’ana masu yawo a yanar gizo
domin bude ido ko neman wasu muhimman bayanai, shi dillalin zai karkatar da
akalarsu zuwa wani shafi domin su sami abinda suke nema. Wato ana alfahari da
kuma samun alkhairi bisa yawan jama’a a shafukan yanar gizo.
Madaba’ar Jaridu ko Mujallu (Publications or Newspapers) :
A halin yanzu jama’a da dama sunfi son su karanta sababbin
labarai da dumi dumin su a yanar gizo fiye da sayen jaridu da mujallu kamar
yadda aka saba. Idan har ya kasance mutum yana da hanyoyin samun labarai
wadanda jama’a suke da bukata a koda yaushe, to sai ya bude shafi a yanar gizo
kuma ya tsara hanyar da jama’a za subi wajen biyan shi hakinsa kafin su sami
damar karanta labaran da suke bukata. Idan mai karatu zai iya tuna yadda kafofin
yada labarai sukan ce sun samo labarai daga babbar tashar dillancin labarai ta
duniya wato Reuters da sauransu.
Kuma za’a iya bada damar karanta labarai kyauta a shafinka
na yanar gizo domin ka sami jama’a masu yawan gaske. Wannan yawan jama’ar ko
kuma maziyarta za’a iya mayar dashi hanyar samun alkhairi ta hanyar karbar
tallace tallace na wasu shafukan ko hajoji kamar dai yadda bayani ya gabata a
cikin tsarin sana’ar dillanci a yanar gizo.
Kasuwancin Hadin Gwiwa (Network Marketing):
Wannan shima wani nau’ine na kasuwanci a yanar gizo, inda
manyan kamfanonin tallace tallace na yanar gizo suke bayar da tallace-tallace
ko dillanci ga matsakaitan ‘yan kasuwa, su kuma sai suyi amfani da wasu hanyoyi
ko dabarun kasuwanci domin jawo hankulan kanan ‘yan kasuwa su karbi talla daga
garesu. Wanda a karshe suna da riba biyu kenan. Suna samun kamasho a duk hajar
da suka sayar da kansu idan wadanda aka baiwa dillanci sukayi ciniki anan ma
suna da wani kaso a ciki, saboda sune sukayi sanadin shigar su. Shiyasa ya zama
kasuwancin hadin gwiwa.
Ma’ana Kasuwanci ne da yake kara bunkasa a yayin da aka jawo
ra’ayin wani ya shigo, akwai kamasho akan hakan. Sannan wanda aka jawo shima
idan yayi ciniki ana kara samun wani kamasho. Shima idan ya jawo wasu ciki
shima haka zaiyi ta samun alkhairi. Ta wannan hadin gwiwa za’ayi ta karuwa ko
bunkasa kasuwanci.
Hada-hadar Kasuwancin kudaden kasar waje (Forex Trade):
A gaskiya wannan nau’in kasuwanci akwai sarkakiya da kuma
wahala wajen aiwatarwa. Yinsa sai wadanda suke da masaniya game da hawa da
saukar darajar kudaden kasashen duniya. Ni a ganina wannan kasuwanci na hada
hadar kudaden waje, yayi kama da sana’ar ‘Yan kasuwar Canji da muke dasu anan.
Idan ana neman Jama’ar da za’a baiwa horo akan irin wannan sana’a cikin
kankanin lokaci kuma su kware akan lokaci to sai ince a nemi ‘Yan Chanji.
Dangane da yadda ake yinsa bashi da maraba da yadda ake
sana’ar chanji a duniyar mu ta zahiri. Kuma a kwai cibiyoyi masu yawan gaske da
ake bada horo akan yadda ake gudanarwa. Masu yin wannan sana’a kullum suna
gaban na’urar kompiyutar su wadda ke kan tsarin wata yawa a yanar gizo, suna ta
hasashe akan riba ko faduwa dake cikin harakar.
A halin yanzu ku jama’a kun isa sheda wajen fahimtar yadda
shafukan bada ilimi suka yawaita a yanar gizo, kama daga na kyauta har zuwa
wadanda sai am biya kudi. A kwai makarantu masu yawan gaske a yanar gizo
wadanda ta shafin yanar gizo dalibai suke daukar darussa, suna daga wata uwa
duniya, a kasashensu, a garuruwansu kuma acikin dakunansu ta hanyar amfani da
kompiyuta da ikon shiga yanar gizo.
Saboda haka Allah kadai shine abin godiya da ya samar damu,
kuma ya samar da hanyoyin cin abinci iri-iri a garemu. Idan Allah Ya baka
ilimi, basira ko hikima to ai yabaka jari mai girman gaske. A kwai fannonin
ilimi wadanda idan mutum ya bude masu shafi a yanar gizo kuma ya tallata wannan
shafin cikin ikon Allah sai ya zama alkhairi a gareshi sannan ya sami ladan
ilimantarwa a wajen Allah. Don haka yana da kyau mutum yayi amfani da damar da
Allah ya bashi akan lokaci tun kafin ta kubce masa.
Idan har kana da gudummawar da zaka bayar a duniya kuma ka
sami alkhairi, kai tsaye ka tafi ka sami masu basirar bude ko gina shafi a
yanar gizo, ku zauna ka sanar dashi dukkan bukatunka. Shikuma zai baka mamaki
wajen tsara maka shafin yanar gizo.
Za’a iya bude shafin yanar gizo domin koyar da sana’o’i
wanda nayi imani za’a sami alkhairi maiyawan gaske. Akwai sana’o’i wadanda idan
akabude masu shafi a yanar gizo za’a sami cigaba da alkhairi maiyawa.
Kadan kenan daga cikin ire-iren sana’o’in da’ake iya
gudanarwa a yanar gizo. Sannan yana da kyau a sani cewa dukkanin wadancan
sana’o’i da muka bayyana a sama, baza a iya aiwatar dasu ba har sai an mallaki
iIlimin fasahar sarrafa na’urar Kompiyuta (Computer) da makamantansu.
Don haka ga duk mai sha’awar yin daya daga cikin wadancan
sana’o’i da muka bayyana kai harma da wadanda bamu fada ba indai a yanar gizo
ake gudanar dasu, kofarmu abude take domin baku shawar wari akan a bubuwan da
suka dace.
Kasuwancin Zamani yana kunshe da nasarori da alkhairai masu
yawa ta fuskoki daban-daban. Yana samar da aiyyuka da kuma kwar da zaman kashe
wando da matasa ‘yam boko masu jiran aikin gwamnati bayan an kare karatu.