Wednesday 3 September 2014

Saurari Maimaicin Shirin Kasuwancin Zamani


Assalamu Alaikum Warahmatullah!

Barkan mu da wannan lokaci. Dafatan Alkhairi a garemu baki daya. Allah ya sada mu da dukkan Alkhairin dake cikin wannan rana, sannan kuma ya kare mu daga dukkan sharrin da ke cikin ta.

Jama'a, masoya da masu sauraron mu ta Radion Gaskiya Dokin Karfe (Express Radio 90.3 FM) da kuma daukacin wadanda ke tare da mu a shafin internet, muna rokon Allah ya saka kowa da Alkhairi a bisa gudummawa, kwarin gwiwa da goyon bayan da muke ta samu daga gareku, Allah Yabar Zumunci.

Sannan kuma munayi muku albishir da cewa a yanzu ansamar da dandali a cikin Babban shafin mu na kasuwancin zamani wanda akayi wa lakabi da "TASKAR MU" domin baku damar sake sauraron shirin kasuwancin zamani da suka gabata har ma da sababbi.Bayan sauraro za' a iya saukewa ma'ana downloading kenan zuwa cikin na'urorin ku.  http://www.kasuwancinzamani.com/taskar-mu/

Sannan muna bada shawara cewa yana da kyau a ringa sabunta kayan aikin (softwares) na'urorin (Kwamfiyutoci da Wayoyi) da ake aiki da su  anan ina nufin aringa Sofware ko Program Updating ke nan.

Kuma hanyar da ake bi ada domin sauraron maimaicin shirin, tana nan daram. Don haka muke kara yiwa Allah godiya, domin shine ya zabe mu wajen gabatar da wannan al'amari, amma ba don munfi kowa sani ba.

Allah Ya Bamu Alkhairi!!!